<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>93</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku mutanen Almasihu,
 Rera waƙa, dukanku.
 Sai ku faɗa wa jama'a
 Duk labarin cetonku.
 Albishir ne, Maryamu
 Ta haife shi, Ɗan Mutum,
 Sai fa godiya ga Allah
 Domin duk alherinsa.

[V2]
 2) Sa'an nan ya ƙara girma.
 Cike da tagomashi,
 Shi Ɗan Allah yana koya
 Mana hanyar adalci.
 Idan mu amintattu ne,
 Idan mun bi sawunsa,
 Za ya kai mu wurin Uba,
 Za mu sadu wurinsa.

[V3]
 3) Wajibi ne sai mu bi shi,
 Domin yawan ƙaunarsa.
 Shi ya sha wahalar giciye,
 Ba don ya yi laifi ba.
 Laifofin jama'a duka
 Suka kai shi mutuwa.
 Ƙofar rai ce shi ya buɗe
 Don ya kai mu fadarsa,

[V4]
 4) Sai in yi masa sujada,
 Allahna da Sarkina.
 Sai in bauta masa kullum
 Da iyakar ƙarfina.
 Sai da dukan hankalina,
 Sai da dukan zuciyata,
 Zan bi Yesu, Mai Cetona,
 Cikin ikon Ruhunsa.</lyrics>
<title>Ku Mutanen Almasihu LW93</title>
</song>